Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - “Muna ganin cewa al’amarin farko na al’ummar musulmi wato Palastinu, ya shiga cikin wani hali na kara rincabewa, Gwamnatin yahudawan sahyoniya suna da yaudara suna kokarin ganin bayan lamarin,” Saeed Khatibzadeh ya fadi hakan a wani taron manema labarai na mako-mako a birnin Tehran.
Ya kara da cewa har yanzu Falasdinu ita ce batu mafi muhimmanci na al'ummar musulmi, ba tare da la'akari da makircin da gwamnatin Tel Aviv ke kullawa a kan hakan ba.
Khatibzadeh ya kuma bayyana cewa, batun Falasdinu shi ne babban lamari mafi fifiko ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma dukkanin kasashe masu son 'yanci da ke adawa da wariya.
Jami'in diflomasiyyar na Iran ya ce; daidaita huldar diflomasiyya tsakanin wasu kasashen Larabawa da Isra'ila ya karfafawa Isra’ila gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da ayyukan ta'addanci.
342/